Labarai
Sojoji sun kwato bindigogi shida a hannun wanda ake zargi da safarar su a Taraba

Rundunar Sojin kasar nan karkashin runduna ta 6 ta Operation Whirl Stroke ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Abubakar Ibrahim mai shekaru 48 bisa zargin safarar makamai a Karamar Hukumar Ibi ta Jihar Taraba.
Hakan na cikin sanarwar da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar, Laftanar Umar Muhammad, ya fitar a jiya Asabar.
Sanarwar ta bayyana cewa jami’an da ke sansanin Forward Operating Base a Wukari ne suka kama shi bayan samun sahihan bayanan sirri, inda suka kwato bindigogi kirar PKT guda shida, harsasai kirar 7.62mm guda biyu, kudi Naira 170,000, mota kirar Peugeot 504 da wayar hannu.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike kan wanda ake zargin, da ta ce nasarar ta taimaka wajen dakile yaduwar makamai ba bisa ka’ida ba a jihar.
Shugaban runduna ta 6, Birgediya Janar Chukwuemeka Micheal Akaliro, ya yabawa sojojin kan yadda suka gudanar da aikin, tare da kira ga jama’a su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro
You must be logged in to post a comment Login