Connect with us

Labarai

Sojoji sun lalata maɓoyar masu garkuwa da mutane tare da ceto mutane takwas

Published

on

Rundunar sojin kasar nan, ta lalata wata maɓoyar masu garkuwa da mutane tare da ceto mutum takwas a dajin Badurum Kasa da ke ƙaramar hukumar Kauru a jihar Kaduna.

 

Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, inda ta ce, sojojin sun lalata moboyar ta su yayin wani samame da suka kai da hadin gwiwar  rundunar ƴansandan Zango Kataf da dakarun sa kai ta CJTF da masu gadin daji da kuma mafarauta.

 

Ta cikin sanarwar, rundunar ta ce, ta samu damar yin samamen ne bayan samun sahihin bayanan sirri kan inda masu laifin ke ɓoye.

 

Sanarwar ta kara da cewa, Sojojin sun yi arangama da masu garkuwa da mutanen inda wasu suka tsere suka bar waɗanda suka sace a baya lamarin da ya sa sojojin suka yi nasarar ceto mutane takwas.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!