Connect with us

Kiwon Lafiya

Sojojin Najeriya na fafatawa da yan kungiyar boko haram a jihar Borno

Published

on

Runsunar sojan kasar nan ta ce, sojojin ta na fafatawa da ‘ya’yan kungiyar Boko Haram wanda suka kai hari kan rundunar dake Baga a karamar hukumar Kukawa dake jihar Borno.

Bayanin hakan na kunshe cikin sanarwar da rundunar ta buga a shafin ta na Twitter cewa sojojin na maida martani kan harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai  wa Bataliya ta 7 dake yankin.

Wannan nan dai shi ne karu na uku da rundunar sojan kasar nan ke maida martani ga kungiyar Boko Haram bayan da suka yi yukurin kan sojojin ta dake Baga.

Da karfe 6 na yammacin jiya Laraba ‘yan tada kayar bayan suka kai hari kan bataliya ta 6 yayin da sojojin suka sami nasarar kashe 7 daga cikin su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,747 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!