Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Fiye da muslmi 500 ne suka taya mabiya addini Kirista murnar Kirisimeti a Kaduna

Published

on

Fiye da muslimai dari 500 ne suka taya ‘yan uwa mabiya addinin Kirista murnar zagayuwar haihuwar Yesu-Al-Masihu a gidan Limamin Majami’ar Avabgelical Pasto Yohanna Burus dake jihar Kaduna, don wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma.

Daga cikin wadanda suka halacci taya murnar akwai matasa da limamai da mata da kungiyoyin kishin al’umma da amsu rike da masarautun gargajiya da suka fito daga  jihohin yakin arewacin kasar nan.

Da yake jawabi a wajen limamin Yohanna Buru ya ce ya ji dadi matuka da yadda ‘yan uwa musulmai suka nuna cewa babu wani bambanci tsakanin su da ‘yan uwan su mabiya addinin Kiristanci.

Ya ce wannan ziyarar taya murnar zai sake karababa wanzar da zaman lafiya da kuma kara son juna a tsakanin mabiya addinai.

Kazalika da yake jawabi a yayin ziyarar taya murnar tsohon shugaban sashin nazari tsirai na kwalejin kimiyya da fasaaha ta jihar ta Kaduna, Dr, Yusuf Nadabo wanda kuma shi ne jaogran matasan ya sake jadada muhimmancin samar da zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai a kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!