Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojojin Najeriya sun dakile wani hari a Kaduna

Published

on

Sojojin Najeriya sun dakile wani yunkurin kai hari a filin jirgin saman Kaduna da safiyar yau Juma’a.

Rahotannin sun bayyana cewa yan bindiga sun kaiwa filin jirgin saman hari sau biyu a cikin makonni biyu da suka gabata, tare da yin awon gaba da mutane 9.

Sai dai kasa da kwanaki biyu Kenan da sako mutane da aka yi garkuwa da su a harin na farko biyo bayan biyan kudin fansa sama da Naira miliyan biyar da dubu dari biyar.

Wata majiya ta shaida cewa, shugaban hukumar kula da zirga-zirgar Jiragen saman ya hango ’yan bindigar a kan babura hanyar shingen filin jirgin da ke kusa da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya da safiyar yau Juma’a kuma nan take ya sanar da hukumar.

Majiyar ta ce zuwan sojojin kasa a helikofta na Sojan Sama na Najeriya sun hana ‘yan fashin kai hari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!