Labarai
Sojojin Sama sun hallaka kusan ƴan ta’adda 600

Rundunar Sojin Saman Najeriya ta tabbatar da hallaka ‘yan ta’adda kusan 600 cikin watanni takwas da suka gabata, waɗanda mafi yawansu a Jihar Borno.
Hakan na cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce, ya na cikin ƙoƙarin da ake yi wajen murƙushe ƙungiyar Boko Haram da sauran masu tayar da ƙayar baya a Arewa maso Gabas.
A cewar sanarwar Hare-haren sun kuma lalata sansanonin ‘yan ta’adda 166 da manyan motocin yaƙi sama da 200.
Haka zalika rundunar tace mafiya yawan hare haren, an kai su ne daga farkon shekarar da muke ciki ta 2025, a jihohin Borno, Yobe da kuma Taraba.
You must be logged in to post a comment Login