Connect with us

Labarai

Sojojin sun kashe ‘yan ta’adda tare da ceto wadanda aka yi garku da su

Published

on

Sojojin ƙasar nan sun kashe ’yan ta’adda da dama tare da kama mutane 24 da ake zargi da laifuka, sannan sun ceto mutane 39 da aka sace a wasu jihohin Arewa cikin mako guda.

Wannan na cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya fitar a ranar Juma’a 13 ga Fabrairu, 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa a Arewa Maso Gabas, rundunar Operation Hadin Kai ta kai hare-hare a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, inda aka kashe ’yan ta’adda da dama, aka kama takwas, sannan aka ceto mutane 11 tare da kwato makamai da kayayyaki.

A Arewa Maso Yamma kuwa, rundunar Operation Fansan Yamma ta kashe wasu daga cikin ’yan ta’adda, ta ceto mutane biyu tare da kwato makamai da dabbobin da aka sace a jihohin Zamfara, Kano da Katsina.

Haka kuma a Arewa Ta Tsakiya, rundunonin Savannah Shield, Enduring Peace da Whirl Stroke sun kama mutane 16, sun ceto mutane 26, tare da kwato makamai da babura a jihohin Kwara, Neja, Filato, Kaduna, Benue, Taraba da Kogi.

Sojojin sun ce za su ci gaba da gudanar da samame domin tabbatar da tsaro a yankunan Arewa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!