Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sulhu Alkhairi ne: Kabiru Gombe ya yafewa Ɗan sarauniya

Published

on

Sakataren ƙungiyar Izala na ƙasa Malam Kabiru Haruna Gombe ya ce, ya yafewa tsohon Kwamishinan ayyuka na Kano injiniya Mu’azu Magaji Ɗan sarauniya.

Wannan dai na zuwa ne, yayin wata ziyara da tsohon kwamishinan ya kaiwa Malam Kabiru Gombe da yammacin Asabar ɗin nan.

Malam Kabiru ya wallafa wasu hotuna a shafin sa na Facebook, har ma ya bayyana cewa “Da yammacin yau Asabar tsohon Kwamishinan ayyuka na jihar Kano Honourable Mu’azu Magaji ya ziyarce mu a gida domin bada hakuri tare da janye kalamansa da yayi a shafin sa na Facebook, ya kuma yi sa’a ya same mu da shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau”.

Malamin ya ci gaba da cewa “Mun yi hakuri, mun yafe masa kuma mun ƙalla zumunci, Allah ya kiyaye gaba”.

Idan za a iya tunawa a Juma’ar nan ne Kabiru Gombe ya bai wa Ɗan sarauniyar wa’adin awanni 12 domin ya fito ya nemi afuwa, kan labarin da ya wallafa game da shi a ranar Alhamis.

A wani saƙo da ya fitar a shafinsa na Facebook, Mu’azu Magaji ya bayyana cewa an samu wata waya da Kabiru Gombe ya ke gindayawa Shugaban APC na ƙasa Mai Mala Buni sharaɗi.

sharuɗin shi ne za su fice daga jam’iyya matuƙar aka shigo da tsohon gwamnan Kano injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso cikin ta.

Sai dai a martaninsa, Kabiru Gombe ya wallafa a Facebook cewa, shi bai taɓa waya da Mai Mala Buni ba, har ma yayi barazanar gurfanar da shi a gaban kotu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!