Labarai
Susa da manjagara: Ganduje ya tsige Ɗansarauniya daga muƙaminsa
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2021/10/WhatsApp-Image-2021-10-12-at-04.45.35.jpeg)
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sauke Injiniya Mu’azu Magaji Ɗansarauniya daga shugabancin kwamitin aikin janyo bututun iskar gas zuwa Kano, wanda aka yi wa lakabi da NNPC/AKK.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito Kwamishinan yada labarai Muhammad Garba ne ya sanar da tsige Mu’azu Magajin a daren jiya Litinin.
Gwamnati ta ce, ta sallame shi ne saboda gazawarsa a aikin da kuma rashin biyayya.
Gwamnan ya umarci shi da ya bada ragamar kwamitin ga mataimakinsa Aminu Babba Dan’Agundi
A watan Afrilun bara ne Gwamna Ganduje ya sauke shi daga muƙamin Kwamishina saboda yin murnar rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa wato Abba Kyari a Facebook.
Daga bisani kuma Gwamnan ya ba shi shugabancin wannan kwamiti.
You must be logged in to post a comment Login