Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ta’addanci: An kama ‘yan sara suka a jihar Bauchi

Published

on

Rundunar ‘yan sandar jihar Bauchi ta yi nasarar cafke ‘yan sara suka su 19, da kuma barayi dauke da muggan makamai.

Kimanin ‘yan ta’adda 20 ne suka kai harin ta’addanci a offishin ‘Yan kwamiti wanda yake kofar Dumi a jihar ta Bauchi, tare da kone mota kirar Hilux, shida.

Lamarin da yayi sanadiyyar konewar wasu daga cikin masu tsaron wajen, kuma tuni aka mika su zuwa asibitin kwararru na jihar Bauchi don kula da su.

Kuma an aike da kwamandan rundunar RSS Swung da tawagarsa zuwa maboyar masu aikata laifi don bincikosu.

Cikin wadanda aka kama sun hada da:

Mubarak Hashim Karofi da Umar Ibrahim inkiya Dan Kwaram da Khalid Ibrahim unguwan Bauchi sai kuma Yahaya Ibrahim Unguwan Bauchi da Mohammed Sani inkiya mai laya Kofar Dumi.

Sauran sune: Abdulmajeed Muktar inkiya Dila Saman karofi da Abubakar Dahiru uguwar Gado Bauchi da Mustapha Muhammed inkiya Maidala Sabuwar Kasuwa sai kuma Suleiman Suleiman mai inkiya da Babaji Kasuwar Fada.

Cikin su dai akwai: Muktar Abdullahi inkiya Junior da Naziru Jibrin mai inkiya da Grap da Musa Bala wanda aka fi sa ni da Army sai Abubakar Bala inkiya Gashi da kuma Isiyaku Adamu inkiya Na Malama sai Nazir Isma’ila inkiya Ola.

Sauran sune: Abubakar Sanusi wanda aka fi sa ni da Abba da damu Ahma inkiya Ado sai Rabi’u Umar inkiya Rabson da Bashir Yahaya mai inkiya da Basho.

Kuma tuni an aike da su zuwa kotu don yanke musu hukunci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!