Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tantance malaman makarantu zai taimaka wajen sanin abinda gwamnati zata biya na Albashi-ES KSSSSMB

Published

on

Shugaban hukumar kula da makarantun sakandire watau Dr Kabir Ado Zakirai ya bayyana cewa tantance malaman makarantu sakandire da gwamnatin jihar Kano ta bullo da shi zai yi matukar tasiri wajen gane malaman da suke zuwa aiki da masu matsalolin da za’a kawo gyaran ilimi a fadin jihar Kano.

Dr Kabi Zakirai ya bayyana hakane ga manema labarai a yayin da ya jagoranci taron tantance ma’aikata da malaman makarantu na kananan hukumokin Gwarzo da Kabo da ya gudana a karamar hukumar Gwarzo a wannan rana ta litinin.

Dr Zakirai yace wannan na da nasaba da tabbatar da dokar kota kwana da gwamna Abba Kabir Yusuf yayi Qasa da Makwanni biyu da suka gabata dan tabbatar samun cigaban ilimi a jihar.

Babban sakataren ya kara da cewa kamar yadda aka fara wannan tantancewa haka kuma wannan zai bada damar sanin adadin malamai da ma’aikatan da suke aiki dan sanin adadin abinda zata biya a bangaren Albashi.

“Kamar yadda muka sani mai girma gwamna yana bakin kokarin sa wajen dawo da martabar ilimi sabanin yadda gwamnatin da ta shude ta baddala shi.”

“A wannan tsari ne zamu gane adadin malamai nawa garemu,sannan wannane zai taimaka wajen gane adadin masu Gadi da Leburorin da muke dasu da kuma yawan su kansu makarantun.

Zakirai yakuma tabbatar da cewa hakan zai bada dama fahimtar adadin malamai da masu Gadi da Leburorin da zata samar ma hukumar dan bunkusa harkar ilimi a makarantu sakandire.

Sai dai Babban sakataren ya bukaci wadanda za’ayi ma Bio Datar dasu zama masu bada hadin kai da goyon baya ga Jami’an da zasu jagoranci wannan aikin tantancewa.

Zakirai ya kuma bayyana irin na’am da malaman da sauran ma’aikatan suka nuna ta hanyar biyan albashin su da ake biya kan lokaci da karin girma na furomoshen.

“Muna kara kira ga al’ummar jihar Kano dasu cigaba da addu’a dan kawo karshen dukkan makarkashiyar Makiya jihar suke kunno Kano.

Suma a nasu bangare jagororin gudanar Bio Data din sun bayyana godiyar su gwamnatin jihar Kano bisa wannan nazari dan ganin an shawo kan matsalolin da suka fi fuskanta tare da nemi hanyoyin da za’a samu gyara.

Haka kuma su bayyana cewa zasuyi aiki bisa koyarwar mai girma gwamna da kwamishinan ilimi da duka jogaran hukumar tasu ta KSSSSMB watau Dr. Kabiru Ado Zakirai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!