Connect with us

Labarai

Tattalin arziki: Buhari ya isa ƙasar Saudiyya

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Riyadh na ƙasar Saudi Arabia.

Shugaba Buhari ya isa birnin ne don halartar taron zuba hannun jari karo na biyar.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ya sauka a filin jirgin saman sarki Khalid a birnin Riyadh da misalin ƙarfe 11 na dare.

Haka zalika ya samu tarba daga tawagar gwamnati da jakadancin ƙasar, baya ga tawagar rakiyar sa da suka haɗar da ministoci da sauran ƴan Najeriya mazauna Saudi Arabia.

Tuni dai sanarwar da mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya fitar, ta bayyana cewa shugaba Buhari zai gabatar da ibadar Umara gabanin dawowar sa gida bayan kammala taron.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!