Labarai
Tattalin arzikin Najeriya na karuwa bayan janye tallafin mai – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya ce gyare-gyaren tattalin arziki da Najeriya ke yi sun fara haifar da sakamako mai kyau.
Rahoton ya nuna cewa tattalin arzikin ƙasar ya bunƙasa da kaso 4% a shekarar 2025, sakamakon ci gaban bangarorin ayyuka kamar sadarwa, harkokin kuɗi da gidaje.
Haka kuma, hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 15.1% a farkon 2026, daga sama da kashi 26% a bara, abin da ya ɗan sauƙaƙa wa jama’a.
Sai dai Bankin ya yi gargadi cewa wannan ci gaba ba shi da ƙarfi sosai, saboda tashin farashin mai da sauran kayayyaki a duniya, musamman rikicin Gabas ta Tsakiya.
Bankin ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya da kada ta yi amfani da karin kuɗaɗen da take samu daga man fetur wajen ba da tallafin mai, sai dai ta fi mayar da hankali kan taimakon talakawa ta hanyar shirye-shiryen tallafi na musamman.
A nan gaba, ana hasashen tattalin arzikin Najeriya zai ci gaba da bunƙasa zuwa kusan kashi 4.2% tsakanin 2026 zuwa 2028.
You must be logged in to post a comment Login