Labarai
Tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kaso 3 da digo 13 cikin 100- NBS

Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS, ta ce, tattalin arzikin kasar ya ƙaru da kaso 3 da digo 13 cikin 100 a watanni uku na farkon shekarar nan da muke ciki ta 2025.
Sanarwar ta NBS ta baya-bayan nan ta ce, wannan ya zarta kaso 2 da digo 27 cikin 100 da aka samu a irin wannan lokaci a shekarar 2024.
Rahoton ya ce ɓangarorin da suka fi ba da gudummawa wajen haɓakar tattalin arziƙin sun haɗa da na ayyuka da kuma masana’antu, kamar yadda shugaban hukumar ƙididdigar ta ƙasa, Adeyemi Adeniran ya tabbatar.
Adeniran ya ƙara da cewa sassa guda biyar da suka fi taka rawa wajen wannan ci gaban sun haɗa da, bangaren noman da kasuwanci da ɓangaren masana’antu da kamfononin sadarwa da kuma man fetur da iskar gas.
You must be logged in to post a comment Login