Labarai
Tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kaso 4.23- NBS

Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS, ta bayyana cewa, tattalin arzikin kasar ya ƙaru da kaso 4 da digo 23 cikin ɗari a ma’aunin tattalin arziki a zango na biyu na shekarar nan da muke ciki ta 2025 idan aka kwatanta da shekarar 2024.
Hukumar ta bayyana haka ne ta cikin rahoton ta na zango na biyu na shekarar 2025 da ta fitar a birnin tarayya a Abuja ,a baya bayan nan.
A cewar rahoton, bangaren noma ya samu ci gaba da kaso sama da 2, idan aka kwatanta da kaso 2 da digo 60 da aka samu a zango na biyu na 2024, ya yin da bangaren masana’antu ya samu ci gaban kaso 7 da digo 45, wanda ya ninka kaso 3 da digo 72 da aka samu a zango na biyu na 2024, sai bangaren ayyuka kuma ya samu kaso 3 da digo 94 idan aka kwatanta da 3 da 83 na zango na biyu na 2024.
NBS ta ce a cikin zango na biyu na 2025, darajar kudaden shiga ta kai Naira tiriliyan 100 da digo 73, idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 84 da digo 48 da aka samu a zango na biyu na 2024, wanda ya nuna ci gaban shekara zuwa shekara da kaso 19 da digo 23.
You must be logged in to post a comment Login