Labarai
Tawagar wakilan Amurka ta iso Najeriya domin bincike kan iƙirarin kisan Kiristoci

Tawagar ‘yanmajalisar Amurka ta iso nan Najeriya a yau Lahadi domin bincike kan sahihancin iƙirarin yi iwa Kiristoci kisan gilla.
mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro malam Nuhu Ribadu ya ce, ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a tasu ziyarar da suka kai birnin Washington a watan Nuwamba da ya gabata.
“Tawagar ta ƙunshi ‘yanmajalisar wakilai Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore,” in ji Ribadu cikin wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta.
Kazalika, Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills na cikin tawagar.
Ribadu ya ce sun tattauna matakan yaƙi da ta’addanaci, da zaman lafiya a Afirka, da hanyoyin ƙarfafa ƙawancen tsaro tsakanin Najeriya da Amurka
You must be logged in to post a comment Login