Connect with us

Labaran Kano

Tilas a magance cin zarafin mata- Mai dakin Sarkin Kano.

Published

on

Mai dakin sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II, Hajiya Maryam Muhammad Sanusi ta bayyana cewa ya zama tilas a magance cin zarafin cikin gida dake faruwa tsakanin ma’aurata.

Hajiya Maryam ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi a taron magance cin zarafi tsakanin iyali da ta shirya yau a fadar sarkin Kano.

Tace  ba wai duka ko zagi ne kadai cin zarafi ba, cusgunawa ta bangaren hantara da kin kula mace, ko kin bata wasu hakkokinta, ba tare da kwakkwaran dalili ba.

“Wannan na daya daga cikin muzgunawa wanda a yawancin lokuta idan mace takai kara sai ace tayi hakuri ta zauna” a cewar Hajiya Maryam Muhammad Sunusi II.

Wakiliyar mu Samira Saad Zakirai ta rawaito cewa mai dakin ta mai marataba sarki Muhammadu Sunusi II tace akwai bukatar duk namijin da za’a yiwa aure to magabatansa su kirashi suyi masa nasiha tare da fada masa hakkokin da suke kansa na matarsa kamar yadda ake bata lokaci wajen yiwa amare.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,834 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!