Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Za’a koyar da fursunoni arba’in karatun Firamare

Published

on

Sama da Fursunoni arba’in da hudu ne zasu fara karatun Firamare a gidan gyaran hali dake Goron Dutse a jihar Kano.

Shugaban hadakar kungiyar masu Koyarda Ilimin manya ta kasa Reshen jihar Kano Alhaji Garba Magaji ne ya bayyana hakan lokacin bikin bude ajujuwan koyar da  mazauna gidan gyaran hali dake Goron Dutse a yau.

Alhaji Garba Magaji ya kara da cewa sun dauki matakin koyarda mazauna gidan gyaran halin ne domin inganta rayuwarsu domin kada suyi zaman banza a gidan.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa karatun kammala firamare din zai dauki watanni uku kacal ana koyar dasu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!