Connect with us

Labarai

Fadar Shugaban Kasa ta ce Tinubu na cikin koshin lafiya bayan tuntube a Turkiyya

Published

on

Fadar Shugaban Kasa ta tabbatar da cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu na cikin koshin lafiya, bayan tuntuben da ya yi yayin ziyararsa a fadar shugaban Turkiyya a birnin Ankara.

Mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai, Suday Dare, ya bayyana cewa shugaban bai samu wani rauni ba bayan faruwar lamarin.

Tinubu, mai shekara 73, ya samu tarba ta musamman daga Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wani bikin maraba da aka shirya a fadar shugaban kasar.

Yayin da yake wucewa gaban jerin sojoji da manyan baki, wani bidiyo da aka wallafa a shafin X na shugaban Turkiyya ya nuna lokacin da shugaba Tinubu ya yi tuntube ya faɗi, inda aka yi gaggawar taimaka masa.

Daga bisani an hango Shugaba Tinubu da takwaransa Erdogan suna ci gaba da tattaunawa ba tare da wata matsala ba, abin da ke nuna cewa lamarin bai shafi lafiyar shugaban kasar ba.

To sai dai butun ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda bidiyon ya yadu cikin sauri, lamarin da ya sa fadar shugaban kasa ta fito fili ta tabbatar wa da al’umma cewa Tinubu na cikin koshin lafiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!