Labarai
Tinubu na da ikon zaɓar mataimakinsa a zaɓen 2027- Mustapha Salihu

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa mai kula da yankin Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da cikakken iko bisa tsarin mulkin ƙasa wajen zaɓar mataimakinsa a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Mustapha Salihu, ya yi wannan jawabi ne a cikin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, kwana biyu bayan da ya tsallake rijiya da baya sakamakon wani hari da wasu fusatattun magoya baya suka kai masa a Gombe.
Lamarin ya faru ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron shugabannin APC na Arewa maso Gabas, inda ake zarginsa da kin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a lokacin da ya ke bayyana goyon bayansa ga takarar Tinubu a 2027.
Sai dai a cikin hirar da aka yi da shi, Salihu ya karyata zargin cewa ya ki ambatan sunan Shettima da gangan, yana mai cewa hakan kuskure ne na rashin fahimta.
Ya ce ko da yake jam’iyya na da damar yin shawarwari kan irin waɗannan batutuwa, amma ikon yanke hukuncin zaɓin mataimaki na zaɓen shugaban ƙasa yana hannun ɗan takara ne shi kaɗai.
You must be logged in to post a comment Login