ilimi
Tinubu na shirin kaddamar da tallafin karatu ga ɗalibai a ƙasashen Gabashin Caribbean

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da kaddamar da wani sabon shirin tallafin karatu ga ɗalibai daga ƙasashen da suka kasance mambobi a kungiyar Kasashen Gabashin Caribbean, domin su samu damar yin karatu a manyan jami’o’in Najeriya.
Ta cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin, ya ce, shirin na daga cikin manufofin gwamnati na bunƙasa haɗin gwiwa a fannin ilimi da karfafa alaka tsakanin Najeriya da ƙasashen Caribbean.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai da ya gudanar tare da Firayim Ministan ƙasar Saint Lucia Philip J. Pierre, a Gros Islet.
Ya ce, shirin zai taimaka wajen gina dangantaka mai ɗorewa tsakanin al’ummomin ƙasashen biyu, tare da bai wa matasa damar cin gajiyar ilimi a matakin ƙasa da ƙasa.
Za dai a fara aiwatar da wannan shiri ne a kakar karatu mai zuwa.
You must be logged in to post a comment Login