Labarai
Tinubu ne zai karɓi Najeriya a 2023 – Abdulmuminu Kofa
Tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Ƙiru da Bebeji Abdulmuminu Jibrin Kofa ya tabbatar da cewa Bola Ahmed Tinibu zai tsaya takarar shugabancin Najeriya a kakar zaɓen 2023.
Abdulmuminu Jibrin Kofa ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin taron manema labarai, jim kaɗan bayan kammala gudanar da addu’a da aka shirya ga ƙasar nan don shigowar sabuwar shekarar 2022.
A cewar Kofa “A halin yanzu babu wanda ya cancanci ya shugabanci Najeriya fiye da Tinibu La’akari da muƙaman da ya rike a ƙasar nan”.
“Babu wani wai wai Tinubu muke yi shi muke tallatawa a jam’iyyar APC shi za mu taimakawa kuma shi muke faɗawa mutanen mu su yi shi, don haka ba mamaki don an ga muna tallansa”.
Da ya ke batu kan sulhu tsakanin tshohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Abdulmuminu Kofa ya ce “Ba abin mamaki ba ne yin sulhu tsakanin kwankaso da Ganduje idan aka yi La’akari da daɗewar da suka yi tare, don haka in sun yi sulhu tsakanin su zai kasance alkhairi ga al’ummar Kano”.
Abdulmuminu Jibrin Kofa ya ce rigingimun da ake samu a jamiyyar APC zai zo ƙarshe ba da jimawa ba.
You must be logged in to post a comment Login