Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda Abdulmumin Kofa ya shirya addu’ar zaman lafiya da yakar Corona a Kano

Published

on

Fitaccen dan siyasa kuma  Babban Daraktan hukumar samar da gidaje ta kasa ya ce  Gwamnatin tarayya  zata cigaba da shirya tarukan addu’oi na malamai don yiwa kasar nan addu’oi na musamman don neman daukin mahalicci kan barazanar tsaro da yankin Arewacin kasar ke fuskanta a yanzu don kawo karshen matsalar.

Abdulmumin Jibrin Kofa ne ya bayyana hakan a ya yin taron addu’oi na musamman da ya shirya wanda aka tara malamai a karamar hukumar Bebeji don gudanar da addu’oi kan matsalolin dake addabar kasar ciki har da dawowar cutar Corona karo na biyu.

Babban Daraktan hukumar samar da gidaje ta kasa ya kara da cewa an shirya taron ne don neman daukin mahalicci kan matsalolin da Najeriya ke fuskanta na rashin tsaro da kuma sake dawowar cutar Corona karo na biyu har ma da matsalar matsin tattalin arziki da kasar ke fuskanta domin shawo kan matsalar.

Kofa yace a kokarin da gwamnatin shugaba Buhari ke yi da gwamnatin Kano a kowanne mataki shi ma zai cigaba da bata tasa gudunmawar wajen tallafawa jama’ar Kiru da Bebeji da ma Kano da kasa baki daya musamman ta fuskar tsaro har ma da yunkin dakile yaduwar cutar Korona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!