Labarai
Tinubu ya ba da umarnin tsaurara matakan tsaro a wasu jihohi

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin karin tsaurara matakan tsaro a manyan yankunan dazuka na jihohin Kwara, Neja da Kebbi sakamakon karin garkuwa da mutane da hare-haren ’yan ta’adda da aka samu a kwanakin nan.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa, a ƙarƙashin sabon umarnin, Rundunar Sojin Sama ta kasa za ta fara gudanar da tsaron sama na awa 24 ba tare da yankewa ba, a cikin zurfin dazukan wadannan jihohi, inda hukumomin tsaro suka nuna cewa su ne manyan mafakar kungiyoyin ta’addanci da masu garkuwa da mutane.
Ana sa ran hukumomin tsaro za su yi aiki tare domin binciko maboyar ’yan bindiga, hana motsin kungiyoyin ta’addanci a yankunan, tallafa wa sojojin kasa wajen kai farmaki da kuma kwato wuraren da aka mamaye.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da alumma ke ci gaba da nuna damuwa kan yawaitar sace-sace da hare-hare a arewa ta tsakiya da arewa maso Yamma a kwanakin nan.
You must be logged in to post a comment Login