Labarai
Tinubu ya bada uamarnin bincike da cafke wadanda suka kai hari a Benue

Shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci daukacin shugabannin tsaro da su gaggauta kamo wadanda ake zargi da kai harin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane sama da 100 a karamar hukumar guma ta jihar Benue.
Tinubu ya bayar da umarnin ne a ziyarar jaje da ya kai jihar ta Benue yayin da yake ganawa da manyan jami’ai a gidan gwamnatin jihar a larabar makon na, inda bayyana takaicinsa kan rashin kama wadanda suka kai harin.
Shugaba Tinubu ya bukaci gwamnan jihar ta Benue Hyacinth Alia, da ya kafa kwamitin zaman lafiya a jihar, wanda zai kunshi tsoffin gwamnonin jihar da dattawa da sarakunan gargajiya da jami’an gwamnatin tarayya da kuma baƙi mazauna jihar domin shawo kan matsalar tsaron da ta jima tana addabar jihar.
You must be logged in to post a comment Login