Labarai
Tinubu ya bai wa Shettima umarnin zuwa Birtaniya domin dauko gawar Buhari

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci mataimakinsa, Kashim Shettima, da ya tafi Birtaniya domin ɗauko gawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zuwa Najeriya, bayan rasuwarsa a London.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan kafafen yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar a yau Lahadi
Sanarwar ta bayyana cewa Buhari ya rasu ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a wani asibiti da ke birnin London, bayan doguwar jinya.
Tinubu ya ce ya tuntubi uwargidan marigayin, Hajiya Aisha Buhari, inda ya miƙa ta’aziyya da gaisuwar juyayi ga iyalinsa da kuma al’ummar Najeriya gaba ɗaya.
An kuma bayyana cewa daga yau tutocin Najeriya za su rika sauka rabin sanda a manyan wuraren gwamnati a matsayin girmamawa ga marigayin shugaban.
Marigayi shugaba Buhari ya mulki kasar nan sau biyu daga 1984 zuwa 1985 a matsayin shugaban mulkin soja, sannan aka sake zaɓensa shugaban ƙasa a jamhuriyya ta huɗu a shekarar 2015 da kuma 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
You must be logged in to post a comment Login