Labarai
Tinubu ya gana da gwamnoni 6 a Abuja

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da wasu gwamnonin jihohi shida a Fadar mulki ta Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja.
Gwamnonin da suka halarci ganawar sun hada da gwamnan jihar Sakoto, Ahmad Aliyu, da Lucky Aiyedatiwa na Ondo da na Jigawa Umar Namadi Danmodi da kebbi Dakta Nasir Idris da gwamnan jihar Kogi Ahmed Usman Ododo da jihar Edo Monday Okpebholo.
Rahotonni sun bayyana cewa, yayin ganawar a fadar shugaban kasa, shugaban Tinubu, ya tattauna da gwamnonin ne kan muhimman al’amuran gudanar da mulki da suka shafi jihohin su da ma Najeriya baki daya.
You must be logged in to post a comment Login