Labarai
Tinubu ya karbi rahoton DSS kan batun satar dalibai

Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS ya kai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu rahoton halin da ake ciki game da sace-sacen ɗalibai da ‘yanbindiga suka yi a jihohin Kebbi da Neja da ke arewacin ƙasar.
Wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun Tinubu, ya fitar ta ce shugaban DSS, Tosin Adeola Ajayi, ya gana da Tinubu ne a jiya Juma’a da dare.
A ranar Litinin ne ‘yanbindiga suka sace ɗalibai mata 25 daga wata sakandare a garin Maga da ke ƙaramar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi da ke arewa maso yamma.
Sai kuma ranar Juma’a wasu ‘yanbindiga suka sace ɗalibai fiye da 300 da malamansu a wata sakandaren da ke Papiri a cikin jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya.
Tuni Tinubu ya soke balaguronsa zuwa taron G20 a Afirka ta Kudu saboda halin matsalar tsaron, kuma ya tura Ministan Tsaro Abubakar Badaru Neja, yayin da Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Matawalle ya tafi Kebbi.
You must be logged in to post a comment Login