Labarai
Tinubu ya tura Kashim Shettima zuwa jihar Kebbi domin jajantawa al’ummar jihar

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura mataimakinsa Kashim Shettima zuwa Jihar Kebbi domin jajanta wa gwamnatin jihar da iyayen daliban Makarantar sakandiren Maga da aka sace a farkon makonnan.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar.
Sanarwar ta ce shugaban kasa ya nuna damuwa kan sace daliban, sannan ya bai wa hukumomin tsaro umarnin gaggawa domin ganin an ceto su cikin koshin lafiya.
Sanarwar ta kuma ce shugaban ya jajanta wa rundunar soji kan mutuwar jami’ansu Brigadier General Musa Uba a Borno yayin aiki.
Tinubu ya bukaci shugabannin al’umma da jama’a a yankunan da ake fama da matsalar tsaro da su rika taimakawa hukumomin tsaro da bayanai domin tabbatar da tsaron yankunansu.
You must be logged in to post a comment Login