Labarai
Tinubu ya tura ministan tsaro Badaru Abubakar zuwa Naija in da aka sace dalibai sama da 200

Gwamnatin Najeriya ta tura babban ministan tsaron ƙasar, Muhammad Badaru Abubakar, zuwa jihar Neja inda aka sace ɗalibai ‘fiye da 200’.
Ƙaramin ministan tsaron ƙasar, Muhammed Bello Matawalle ne ya bayyana haka ranar Juma’a da maraice a cikin shirin Ra’ayi Riga na BBC Hausa.
”Shi ma Badaru zai je Neja kamar yadda aka turoni Kebbi, domin ƙoƙarin gwamnati na kuɓutar da ɗaliban da aka sace”, in ji shi
Tuni dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tura ƙaramin ministan tsaron zuwa jihar Kebbi – inda ƴanbindiga suka sace ɗalibai ƴanmata 25 – domin sanya idanu kan ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban.
You must be logged in to post a comment Login