Labarai
Tinubu ya umurci masu shi’awar takara a 2027 su yi murabus daga mukaman su na siyasa

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya umurci dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa da ke da niyyar tsayawa takara a zaɓen 2027 su ajiye mukamansu kafin ko a ranar 31 ga Maris, 2026.
Wannan umarni ya shafi ministoci, masu ba shugaban ƙasa shawara, mataimaka na musamman, da shugabannin hukumomin gwamnati da sauran mukaman siyasa.
Sanarwar ta fito ne daga ofishin George Akume, Sakataren Gwamnatin Tarayya, inda aka ce wannan mataki ya dace da sashe na 88(1) na dokar zaɓe ta 2026, tare da jadawalin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar domin shirye-shiryen zaɓen 2027.
An kuma umurci duk wanda abin ya shafa da ya miƙa takardar murabus dinsa kafin wa’adin da aka ƙayyade.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa wannan doka na da muhimmanci domin tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin siyasa, tare da hana amfani da iko wajen samun riba a zaɓe. Ya kuma jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya da tabbatar da sahihin zaɓe a ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login