Labarai
Tinubu zai halarci taron zuba jari na ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje

Shugaban ƙasa Tinubu, zai halarci taron zuba jari na Najeriya nan mazauna ƙasashen waje karo na takwas matsayin bako na musamman, wanda za a gudanar daga ranar 11 zuwa 13 ga watan Nuwamban 2025 a Abuja.
Shugabar hukumar kula da ’yan Nijeriya mazauna ƙetare NiDCOM’l, Abike Dabiri-Erewa ce ta sanar da hakan yayin taron manema labarai kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Abike ta ce, tun bayan fara taron a 2018, an samu karuwar zuba jari daga ’yan Nijeriya da ke ƙasashen waje a fannoni kamar gidaje, kiwon lafiya, noma, fasahar sadarwa, makamashi, masana’antu da harkokin kirkire-kirkire.
Dabiri-Erewa ta kara bayyana cewa, a taron bara na 2024 an cimma yarjejeniyar zuba jari da ta kai kimanin naira miliyan 673 a fannoni daban-daban.
You must be logged in to post a comment Login