Labarai
Tinubu zai kai ziyara zuwa Birtaniya

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu zuwa Kasar Birtaniya daga ranar 18 zuwa 19 ga Maris, 2026, bayan samun gayyata ta musamman daga Sarki Charles na Uku. Rahotanni sun nuna cewa Sarki Charles da Sarauniya Camilla za su karɓi Shugaban kasar Nijeriya a Windsor Castle.
Sanarwar da fadar sarautar Birtaniya ta wallafa a shafinta na X ta bayyana cewa Shugaba Tinubu zai tafi tare da matarsa kuma Uwargidan Shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu. A cewar sanarwar, ziyarar za ta gudana daga Laraba 18 ga Maris zuwa Alhamis 19 ga Maris, 2026.
Mai bai wa Shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya ce wannan ita ce ziyara ta farko da wani shugaban Nijeriya zai kai Birtaniya cikin shekaru 37. Ziyarar karshe makamanciyar haka ta gudana ne a shekarar 1989, lokacin da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya kai ziyarar aiki inda marigayiya Sarauniya Elizabeth ta Biyu ta karɓe shi.
You must be logged in to post a comment Login