Labarai
Tinubu zai nada sabbin jakadun Najeriya a kasashen ketare

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin fitar da jerin sunayen jakadu da za su wakilci Nijeriya a manyan kasashe cikin makonni masu zuwa, a cewar majiyoyi daga fadar shugaban kasa.
Wannan mataki na zuwa ne bayan damuwar da jama’a ke nunawa kan yadda rashin jakadu ya rage karfin diflomasiyyar Nijeriya, musamman a kasashen da ke da muhimmanci ga hulɗar ƙasa da ƙasa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Tinubu yajanye dukkan tsoffin jakadu a watan Satumban 2023 domin sake fasalin manufofin ƙasar a ketare, sai dai jinkirin tantance sababbin jakadu ya kai shekara biyu ba tare da sabbin nade-naden ba
You must be logged in to post a comment Login