Labarai
Tsadar Rayuwa : Yadda kayayyaki suka yi tashin gwauron zabi a Najeriya
Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce hauhawar farashin kayayyaki a watan jiya na Nuwamba ya kai kaso goma sha hudu da digo tamanin da tara.
Hukumar ta NBS ta bayyana hakan ne ta cikin rahoton da ta saba fitar game da hauhawar farashi a yau talata.
A cewar hukumar hauhawar farashin ya zarce na watan shekaran jiya na Oktoba wanda ya tsaya akan kaso goma sha hudu da digo ashirin da uku.
Hukumar kididdiga ta kasar ta kuma ce a birane farashin ya karu da kaso goma sha biyar da digo digo arba’in da bakwai, yayin da a yankunan karkara ya tsaya a kaso goma sha hudu da digo talatin da uku.
You must be logged in to post a comment Login