Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaftar muhalli: An cafke madara mara inganci a Kano

Published

on

Kwamitin kar-ta-kwana na tsabtar muhalli a jihar Kano, ya kama wata mota makare da madara ba tare da lambar sahalewar hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ba.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso tare da tawagarsa ne suka kama motar, lokacin da yake jagorantar duban tsaftar muhalli na karshen wata.

ya ce, madarar an shigo da ita kasar nan ne daga ketare, kuma tuni an aike da motar zuwa ma’aikatar muhalli, don tattaro masu ruwa da tsaki kan matsalar tare da daukan hukunci akai.

Ya kuma ce, ko a makon da ya gabata ma’aikatar ta kama wasu lemukan roba da sabulai da garin kwaki da wa’adin aikin su ya kare tuntuni kuma ake ci gaba da sayarwa al’umma.

Dakta Kabiru Ibrahim Getso, ya ce, da zarar sun kammala bincike za a gurfanar da masu kayan gaban kotu don hukuntasu.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!