Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaftar muhalli: An ci tarar kasuwar ƴan kaba Naira dubu ɗari 200

Published

on

Kotun tafi da gidanka kan tsaftar muhalli ta yankewa shugabannin kasuwar ƴan kaba tarar Naira dubu ɗari biyu.

Da safiyar ranar Asabar ne kotun wadda ke ƙunshe a cikin tawagar duban tsaftar muhalli ta yanke musu hukuncin

Wannan dai ya biyo bayan samun kasuwar tana ci daidai lokacin da ake tsaka da tsaftar muhalli.

Da yake yanke hukuncin mai Shari’a Auwal Yusuf Sulaiman ya yi sammaci shugabannin kasuwar nan take, tare da yanke tarar Naira dubu ɗari biyu.

Haka kuma kotun ta buƙace su da su gurfana gabanta don amsa tambayoyi tare da biyan tarar.

Bayan kammala duban tsaftar muhallin kuma kotun ta bada Belin Shugaban kasuwar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!