Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaftar Muhalli: Dole a zamanantar da kasuwar ƴan Lemo – Nasiru Garo

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, dole a zamanantar da kasuwar ƴan Lemo da ke Na’ibawa domin tafiya daidai da zamani.

Haka kuma an buƙaci kasuwar da su kula da tsaftar muhallin su don gudun bazuwar cutukan da za a iya kamuwa da su sakamakon shan kayan marmari marasa tsafta.

Kwamishinan muhalli Nasir Sule Garo ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, lokacin da yake duban tsaftar muhalli a kasuwar ta Ƴan Lemo da tashar Na’ibawa da kuma Kano Line.

Ya ce, akwai buƙatar samar da sabon tsari a kasuwar la’akari da ƙaratowar watan azumin Ramadan, wanda al’umma ke yawaita sayen kayan marmari domin yin buɗa baki.

Nasir Sule Garo ya kuma ce, akwai buƙatar zamantantar da harkokin kasuwar ƴan lemo kasancewar kasuwa ce ta kayan da suke saurin lalacewa.

Yana mai cewa, za a yi zama na musamman da shugabannin kasuwar don fito musu da tsare-tsaren inganta kasuwancinsu, domin kuwa akwai buƙatar hakan.

Nasir Sule Garo ya nuna takaici kan yadda ya tarar da wasu ƴan kasuwa suna wanke kayan marmari a harabar banɗaki, yayin da a gefe guda kuma kasuwar bata da wani kebantaccen waje da za a riƙa zubar da lalatattun kayan marmarin.

A nasa bangaren shugaban kasuwar ƴan leko safiyanu Abdullahi ya tabbatar da cewa za su bada goyon baya ga duk tsarin da gwamnati ta zo musu da shi.

Haka kuma a dai ranar ta Juma’a ne mai kotun tafi da gidanka kan harkokin tsaftar muhalli ƙarƙashin mai Shari’a Auwal Yusuf ta rufe wani banɗaki a tashar mota ta Kano line saboda rashin tsafta da ke barazanar yaɗuwar cutuka.

Nasir Sule Garo ya gargaɗi masu ababen hawa da su guji karya dokar tsaftar muhalli a gobe Asabar, yayin da ya bukaci su da suyi amfani da lokacin wajen gyaran muhallansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!