Labarai
Tsaftar Muhalli: Za mu zamanantar da aikin kwasar bahaya a Kano – Gidan Kowa da Akwai
Ƙungiyar masu kwasar bahaya a Kano mai taken “Gidan Kowa da Akwai” za ta samar da sababbin dabarun aikin kwasar masai a Kano.
Shugaban ƙungiyar Alhaji Auwalu Wada Garba ne ya sanar da lokacin da suka gudanar da taron ƙarawa juna sani, wanda wanda ƙungiyar Water aid da Ma’aikatar Muhalli ta Jiha suka shirya ga masu kwasar masai.
Shugaban ya ce “Taron yazo a lokacin da ya dace, domin mun gamsu ainun da sabbin dabaru na zamani da aka nuna mana domin kyautata sana’ar mu”.
Alhaji Auwalu ya ce za su zamanantar da sana’ar su da nufin inganta mahalli da kuma tabbatar da kare lafiyar al’umma.
A jawabin sa kwamishinan Muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso wanda ya samu wakilcin daraktan gudanarwa Sha’aya’u A. Jibril ya ja hankalin mahalarta taron da su yi amfani da ilimin da suka samu domin fito da sababbin dabaru na kwasar bahaya.
Har ma ya ce, zamanantar da aikin kwasar bahaya zai taimaka wajen kyautata muhalli, kuma gwamnati za ta basu gudunmawa.
You must be logged in to post a comment Login