Labarai
Tsaro: Muna bukatar a bai wa jamai’an tsaron jami’o’i lasisin rike makamai – SSANU
Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i ta kasa SSANU ta bukaci gwamnatin tarayya da ta bai wa jami’an tsaron da ke kula da jami’o’i lisisin rike makamai don samar da tsaro.
Shugaban kungiyar na kasa Mohammed Ibrahim Haruna ne ya bukaci hakan yayin zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron kungiyar a birnin tarayya Abuja.
A cewar sa, matukar aka bai wa jami’an tsaron jami o’i lasisin rike makamai da suka hadar da bindigogi zai taimaka wajen magance matsalolin tsaron da suke fuskanta da taimaka musu wajen gudanar da ayyukan su.
Mohammed Ibrahim Haruna ya kalubalanci gwamnatin tarayya kan yadda ta ke wasarere da biyan bukatun ma’aikatan manyan makarantun kasar nan duk da yarjejeniyar da aka kulla da ita.
Yana mai cewa, wannan ne ma ya sanya kungiyar ta fara shirin sake tsunduma yajin aiki nan bada dadewa ba.
You must be logged in to post a comment Login