Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan bindiga sun kashe tsohon jojin babbar kotun jihar Enugu

Published

on

Hukumar ‘yan sandan jihar Enugu ta kaddamar da fara farautar wadanda suka kashe tsohon jojin babbar kotun jihar.

A ranar Lahadi 30 ga watan Mayun 2021 wasu ‘yan bindiga suka kashe tsohon jojin mai shari’a Stanley Nnaji.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Enugu CP Muhammad Aliyu ya fitar na cewa, kawo yanzu ba a kaiga gano wadanda ake zargi da aikata laifin kisan ba.

CP Muhammed Aliyu ya kuma ce hukumar za tayi iya bakin kokarinta wajen ganin an kamo wadanda suka kashe tsohon jojin don su girbe abinda suka shuka.

Rahotanni na cewa, a shekarar 2007 aka dakatar da tsohon jojin babbar kotun ta jihar Enugu mai shari’a Stanley Nnaji sakamakon yanke hukuncin tsige gwamnan jihar Anambra na wancan lokacin da yayi Chris Ngige.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!