Connect with us

ilimi

Tsaro: Muna ci gaba da kwashe ɗaliban mu daga Jos – El-rufa’i

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce, ta fara kwaso ɗalibai ƴan asalin jihar da ke karatu a jami’ar Jos da sauran kwalejojin ta zuwa gida.

Shugaban hukumar bada tallafin karatu a jihar Malam Hassan Rilwan  ne ya bayyana hakan a Alhamis ɗin nan, ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce, kwaso ɗaliban ya biyo bayan yadda jihar ke ci gaba da fuskantar matsalaolin tsaro a kwanakin nan, wanda kuma tuni gwamnatin jihar ta bada umarnin a fara kwaso su zuwa gida.

Malam Hassan Rilwan ya kuma ce, tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne aka fara jigilar ɗaliban daga Jos zuwa jihar Kaduna, kuma za a kammala aikin a ƙarshen makon da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!