Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsawa ta faɗo kan matasa da ke selfie tare da hallaka mutane 38

Published

on

Rahotanni daga kasar Indiya sun ce tsawa ta faɗo kan wasu jama’a wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane talatin da takwas a wasu jihohi biyu da ke ƙasar cikin awanni ashirin da huɗu da suka gabata.

 

Aƙalla mutane goma sha ɗaya sun rasa rayukansu a jihar Rajashtan da ke yammacin ƙasar bayan da tsawar ta faɗo musu aka.

 

 

Babban jami’in ƴan sandan yankin, Ananda Srivastava, ya ce, mafi yawa na waɗanda suka mutun suna tsaka da ɗaukar hotunan selfie ne lokacin da tsawar ta faɗo musu aka.

 

Ya kuma ce wasu mutane tara sun rasa rayukansu lokacin da wata tsawar ta daban ta faɗo musu, kusa da inda ta farkon ta faɗo sannan mutane ashirin sun jikkata.

 

A jihar Uttar Pradesh kuwa mutane goma sha takwas sun rasa rayukansu bayan da tsawar ta faɗo musu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!