Connect with us

Labarai

Tsofaffin Shugabanin Kwamin riko sunyi karar Gwamnan Bauchi

Published

on

Tsofaffin Shugabannin kwamitin riko na kananan hukumomin jihar Bauchi guda Ashirin sun gurfanar da gwamnan jihar Sanata Bala Muhammed gaban kotu bisa zargin sa da sallamar su batare da wa’adin su ya cika ba.

Tsohon shugaban kwamitin riko na karamar Hukumar Bauchi Alhaji Chindo Abdu ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Bauchi.

Ya ce sun gurfanar da gwamnan gaban kotu ne domin tursashi dawo da su ofishin su.

A cewar sa, tsohon gwamnan jihar ta Bauchi Barista Muhammed Abdullahi Abubakar ne ya nada su na tsawon wa’adin watanni tara, wanda lokacin su zai kare ne a watan Satumban bana.

Alhaji Chindo Abdu ya kuma ce bayan karbar rantsuwar kama aiki gwamnan jihar ta Bauchi Sanata Bala Muhammed ya ba da sanarwar sallamar dukkannin nade-naden da tsohon gwamnan da ya gajeshi ya yi.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!