Connect with us

Labarai

Kamfanin NNPC sun fara safarar man fetur kasashen Burkina Faso da Mali da Cote d’Ivore

Published

on

Kamfanin mai na kasa (NNPC), ya ce, masu fasakwaurin man fetur a kasar nan suna safarar sa zuwa kasashen Burkina faso da Mali da kuma Cote d’Ivoire.

 

A cewar kamfanin na (NNPC), ‘yan fasakwaurin suna kuma safarar man fetur din zuwa kasar Ghana domin sayar da shi su ci riba.

 

Babban jami’in gudanarwar kamfanin na NNPC Henry Ikem-Obih ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.

 

Ya ce, yayin da ake sayar da farashin Litar man fetur akan naira dari da arba’in da biyar a kasar  nan a sauran kasashen da ke makwabtaka da kasar nan, ana sayarwa akan naira dari uku da hamsin da kuma dari hudu da talatin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!