Labarai
Tsoffin shugabannin Najeriya tare da shugaba Tinubu za su halarci jana’izar Buhari

A nasa ran tsofaffin shugabannin Najeriya tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu za su halarci jana’izar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yau Litinin a garin Daura da ke jihar Katsina.
Rahotonni sun bayyana cewa za a kawo gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari mahaifarsa Daura da safiyar yau.
Tun a jiya ne dai shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa Kashin Shettima da ya jagoranci dawo da gawar tsohon shugaban kasar daga birnin London zuwa gida Najeriya domin yi masa jana’iza.
You must be logged in to post a comment Login