Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

WAEC: Mun dage lokacin rubuta jarrabawar ta 2021

Published

on

Hukumar shirya jarabawar yammacin Afrika WAEC, ta ce ta dage lokacin rubuta jarrabawar daga watan Yuni da Yuni na shekarar 2021 zuwa wata Agustan 2021.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Demianus Ojijeogu ya fitar, na bayyana cewa jarabawar da aka shirya tun farko a watan Mayu zuwa Yuni, yanzu za ta gudana tsakanin 16 ga watan Agusta zuwa 30 ga Satumbar 2021.

Hukumar shirya jarabawar ta karyata rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke cewa an dage jarrabawar a Najeriya a shekarar 2021.

A cewar sanarwar, matakin ya biyo bayan illar cutar COVID-19 da har yanzu aka gaza samun daidaito a fannin ilimi, sakamakon yadda ta gurbata Kalandar jadawalin tsarin karatu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!