Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Manoma sama da miliyan 5 a Najeriya sun yi rijistar samun tallafi noma – Buhari

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta ce ta yi wa manoma akalla sama da miliyan 5 rajista a duk fadin kasar a kokarin da take na kusanto su ga gwamnatin.

Ministan Noma da raya karkara Alhaji Sabo Nanono ne ya bayyana hakan yayin taron majalisar Manoma da kungiyar Manoma ta Kasa AFAN ta shirya a Kano.

Ministan ya ce, kokarin an yi shi ne don ganin an kawo manoma na kwarai kusa da gwamnati don su ci gajiyar tallafin gwamnati kai tsaye.

Na-nona ya kuma yaba wa kungigyar AFAN kan shirya babban taron Manoma, inda ya bukaci shugabannin kungiyar na kasa su dauki dukkan mambobinsu a matsayin abokan shawara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!