Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wani dan gwagwarmaya zai bi kadin yadda aka yi wa yarinya fyade

Published

on

Wasu yara biyu ne ‘ya’yan manya domin guda daga cikin su dan gidan wani babban dan siyasa ne anan Kano wanda tun zamanin ba ya ake damawa da shi, gagarabadau ne a siyasa domin sunansa ya yi amo, mukamai kuwa ya rike da dama domin yanzu haka ya na da babban mukami a gwamnati cikin nade-nade da aka yi a ‘yan kwanakin nan.

Rahotanni sun nuna cewar wannan yara sun kama wata yarinya ne mai shekaru 7, samfurin kamun daukar amarya, su ka shigar da ita cikin wani shago, a yankinsu dake can wata unguwa wacce sunanta yayi kama da Tudun masu kiwon shanu, unguwa ce da ta ke dab da sunan bishiyar nan mai kama da magarya wato kusa da unguwar rijiyar wani abin marmari na yau da kullum.

Yaran sun yi wa yarinyar barazana da wuka har ta kai sun ma ta fyade, domin har sai da su ka yanke ta a dan yatsanta a kokarin rikicin lallai sai sun biya muguwar bukatar su.

An yiwa daya daga yaran Kano da aka sace fyade

Gwamnatin Gombe ta koka kan yadda ake aikata laifukan fyade

Ya zama wajibi shugaba Buhari ya kawo karshen cin zarafin Musulmi- Kungiya

Daga bisani ne labarin ya fasu amma wata majiya daga unguwar take shaidawa inda ranka cewar, ai babu abin da za a yi wa yaran domin ‘ya’yan manya ne, kuma fa a iya cewar kusan hakan ce ta faru, domin duk wani kokari na samu bayani daga mahaifin yarinyar abin ya gagara, domin a lokacin da mu ka tuntube shi ya shaida mana cewar, su fa sun daidaita da wancan babban dan siyasa wanda unguwar su daya, a unguwar da ake kira da tudun masu korar shanu.

Mahaifin yarinyar ya ce, su ko kadan ba sa bukatar a daga wannan zance domin tsautsayi ne kuma ya faru ya wuce. Duk wani kokari na nusar da shi muhimmancin tsayawa ayi adalci domin a kiyaye gaba bai fahimta ba, ya ma shiga rokon ayi shiru abar Kaza cikin gashinta.

To amma ga ‘yan gwagwarmaya masu fafutukar bin hakkin bil adama, irinsu comrade IG Maryam sun tabbatar da cewar, za su cigaba da bin diddigin wannan Magana domin tabbatar da adalci.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2020/01/COMRADE-IG-MARYAM.mp3?_=1

Barrista Nibras Tahir Jalalain, lauya ce mai kokarin tabbatar da adalci kuma mataimakiyar shugabar kungiyar lauyoyi mata ta duniya reshen jihar Kano, ta ce, za su yi tsayuwar gwamen jaki domin ganin an yi adalci an raba yari da barawo.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2020/01/BARISTA-JALALAINI.mp3?_=2

Tuni dai filin Inda Ranka ya yi arba da binciken likita a kan wannan batu inda likitoci su ka tabbatar da barnar da aka yiwa wanan kankanuwar yarinya, hakan ya sa za mu ji matsayin rundunar yansandan jihar kano anan gaba.

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!