Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wani gwamna ya nada mataimaka ga matan sa uku

Published

on

Gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar ya nada masu taimakawa na mussamam ga matansa guda uku.

 

Daga cikin masu bada shawara na musamman guda 51 da Gwamna badaru ya nada, uku daga cikin an nada su ne a matsayin masu bada shawara na musamman dangane da fitilun tituna da kuma masu kokarin kayyade yawan alumma.

 

A wata takarda da aka fitar dauke da sunayen masu bada shawarar da Gwamnan Jigawan ya fitar, ya nuna cewar Sa’adatu Bashir Muammad ita ce mai bada shawara ga matar Gwamna ta farko, sai Mariya Muhammad Mukhtar ga matar Gwamna ta biyu sai kuma Aisha Garba ga matar Gwamna ta uku .

 

An dai bayyana ayyukan kowanne  mai bada shawarar ga Gwamnan amma banda masu baiwa  matan Gwamnan shawara.

 

Jaridar Daily Trust  ta rawaito cewa ya zuwa yanzu dai ba’a bayyana ayyukan na masu baiwa matan Gwamna shawarar ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!